WATA SABUWA – Ko a sanar da sakamakon zabe dai dai ko a sake zabe – Atiku

Ko a sanar da sakamakon zabe dai dai ko a sake zabe – Atiku

Daga Aliyu Mustapha

Da yammacin jiya Litinin ne lauyoyin dan takaran shugaban kasa a karkashin jam’iyyar PDP a zaben da ya gabata, Alhaji Atiku Abubakar, suka shigar da kara kotun sauraron koken zabe.

Karar na dauke ne da bukatu biyu: na farko, kotu ta sanar cewa Atiku ne ya lashe zaben da ya gabata, ba Buhari ba bisa la’akari da abin da lauyoyin suka kira ‘tulin hujjojin da ke tabbatar da haka’. Na biyu, in hakan bai yiwu ba, to, a soke zaben shugaban kasa da ya gabata.

Jagororin lauyoyin sun hada da Mista Chukwuma Machukwu Ume, Cif Mike Ozekhome, da Mista Emeka Etiaba, dukkansu manyan lauyoyin Nijeriya ne, (SAN). Daga cikin ‘yan siyasan da suka yi mu su rakiya akwai Injiniya Buba Galadima da Kakakin jam’iyyar PDP Mr. Kola Ologbodiyan.

Mai ba wa jam’iyyar PDP shawara a harkar shari’a, Emmanuel Enoidem, ya shaida wa manema labarai cewa: “Muna da manyan lauyoyin Nijeriya guda 20 wadanda gwanaye ne a harkar kararraki a kan zabe, da kuma sauran manyan lauyoyi da ke aiki tare da su. Kazalika muna da shaidu har guda 400 wadanda za su ba da shaida kan wannan kara da muka shigar.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *