Kusanar da wanda ya lashe zaben Kano – Tofa
Daga Aliyu Mustapha
Shahararren dan siyasar nan na Najeriya, Alhaji Bashir Othman Tofa ya yi kira ga ‘yan takarar zaben gwamna a jihar Kano da su yarda da kaddara tsakaninsu duk wanda ya fadi zabe.
Alhaji Bashir Tofa wanda ya kasance shugaban wata kungiyar ci gaban Kano, ya nuna fargabar tashin hankali a Kano idan har aka nemi sauya sakamakon zaben da za a sake a wasu mazabu na jihar.
A hira da yayi da shafin BBC yace: “Yanzu hakkin INEC ne ta fitar da abin da yake shi ne halal wanda za a yadda da shi ko da an tafi kotu.”
Ya kuma yi kira ga ‘yan takarar manyan jam’iyyun siyasar Kano da su ja hankalin magoya bayansu domin ganin an gudanar da zaben lafiya.
A ranar Asabar 23 ga watan Maris ne hukumar INEC ta ce za ta sake yin zabe a wasu mazabu a Kano bayan sanar da cewa ba a kammala zaben jihar ba da aka gudanar a ranar 9 ga Maris.
Duniyarmuayau.com.ng ta rahoto cewa Kungiyar Kano Concerned Citizens Initiative (KCCI) ta bukaci hukumomin tsaro da su zama cikin shiri daga yanzu har zuwa kaddamar da sakamakon zaben da za a sake a jihar.
Shugaban kungiyar, Alhaji Bashir Tofa tare da sauran mambobin kungiyar sun yi wannan kiran yayinda suke jawabi ga manema labarai a ranar Litinin, 18 ga watan Maris a Kano.
Tofa ya bayyana cewa kungiyar KCCI ta jajirce wajen tabbatar da cewar an magance duk wani aiki da ka iya tayar da rikicin siyasa, kafin, lokaci da kuma bayan zabe.