Anbukaci  Matan Nijeriya su shiga adama dasu a siyasan Kungiyar Matan Afirika

Anbukaci  Matan Nijeriya su shiga adama dasu a siyasan

Kungiyar Matan Afirika

Daga Zubairu  M.Lawal

Anbukaci  Shugabannin matan Nijeriya  dasu ri}a shiga ana damawa dasu cikin harkokin siyasan }asanan. Da take Magana a madadin Shugaban Matan Afirika Misis Comfort Lamptey tace; mata a nijeriya suna da gudumawar da zasu bada a harkokin cigaba a siyasan Nijeriya.

Tace; cikin kasha hamsin na masu kada kuri’a a Nijeriya matane, kuma mata basu cin gajiyar siyasa idan aka kafa Gwamnati. Saboda haka ta bukaci matan Nijeriya da suka zama wani abu a harkin siyasa dasu dage su ri}a tsayawa takarar kujeru manya bas u tsaya kawai sai an kafa Gwamnati ake basu mu}ami ba.

Tace; idan mace tana Shugabanci ana samun cigaba masamman ga kowani  bangare, kuma anfi samun cigaba wajen gina }asa.tace; Kungiyar Mata ta nahiyar Afirika tana wayar dakan Mata dasu ri}a himmatuwa wajen tsayawa takara saboda suri}a bada gudumawa wajen gyarar }asa basu  ri}a tsayawa baya sai an kafa Gwamnati ake basu }ananan mu}amai ba.

Ta }ara da cewa kuskurene mata keyi na kin tsayawa ta kara alhalin sune ya kamata su wakilci alumma a gurare dabam dabam saboda sunfi kowa tausayi da sanin yakamata.

Tace; mata da matasa suna bada gudumawa sosai wajen cigaban harkokin siyasa amma idan aka kafa Gwamnati sune ake bari a baya.

Ta }ara da cewa mata sunfi kowa iya tafiyar da harkokin yakin niman zabe saboda mata suna yakin niman zabe cikin nutsuwa da kwanciyar hankali.

Tace; idan mace ke mulki tanada adalcin raba mu}amai kashi hamsin- hamsin ta yadda za’a dama da kowa . ta kara da cewa a zabukar da suka gudana mata nawane suka samu tsayawa takarar kujerun Gwamnoni dana Shugaban }asa?

Itama a nata jawabin Dakta Tunji Ashaolu tace; lokacine da mata ya kamata muyi dammara ana gogawa damu cikin harkokin niman munyan Kujeru kuma a manyan Jami’iyyu ba }anana ba.

Tace; muna da ilumi da hikimomin da zamu iya tafiyar da mulki yadda zamu gyara }asan nan. Dakta tunji tayi kira ga Shugabanni da masu fada aji na Jam’iyyu cewa kamata yayi su ri}a baiwa mata takara na manyan kujeru saboda duk abinda maza zasuyi mata suna iyayin fiye da hakan. Ta }ara da cewa ko a }as ashen turai mata ana damawa dasu wajen ri}e manyan mu}amai a }asa kuma ana yabawa da ayyukansu.

Idan mace tana Shugabanci zata iya samar da zaman lafiya  da tsaro mai inganci a }asa da hadin kan alumman }asa. Da samar da ayyukanyi ga matasa da inganta harkan ilumin yara da kula da tarbiyansu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *