AN KAIWA DAN TAKARAR SANATAN PDP NA KADUNA HARI

Wasu ‘Yan Bangar Siyasa Sunyi Yunkurin Hallaka Mr LA a Kotu

Daga Wakilinmu
A safiyar yau asabar ne kotun dake sauraron korafe korafen zaben 2019 ta cigaba da sauraron karar da akeyi na kujerar majalisar dattwa shiyyar Kaduna tsakiya tsakanin lawal Adamu Usman Mr LA na jam’iyyar PDP da Uba Sani na jam’iyyar APC.
Daman dai ko a zaman kotun a makon da ya gabata, lauyan da ke kare Mr LA barrister Yunus Ustaz ya koka a kan matsin lanbar dayake fuskanta daga bangaren jami’an tsaro, Wanda suka ce Uba Sani yasa a tuhume shi akan sahihancin wasu muhimman bayanan da ya gabatar a gaban kotu. Alkali ya bada umarnin kar wani jami’in tsaron da yakara gayyatarsa har sai bayan ankammala shari’ar da akeyi
Bayan cigaba da sauraran karar na yau inda Lawal Adamu Mr LA yazo kotun domin bada shaidar sa na cewa uba Sani bai ajiye aikinsa da yakeyi na gwamnati kamin Yayi takara kamar yadda doka ta tanada ba. Mr LA Ya kawo wasu takardu kotu da suka nuni da albashin da Uba Sani ya karba na watan junairu da fabarairun shekarar da muke ciki, da kuma wasu takardun da yasa hannu a madadin gwamnatin jihar Kaduna lokacin zaben 2019 da ya gabata. Bayan Mr LA ya kammala amsa tanbayoyin lauyoyin da ke kare jam’iyyar APC da hukumar zabe ne sai Alkalin yace yasamu wuri ya zauna.
Ana cikin haka sai lauyan dake kare Mr LA Ustaz yunus ya gaya wa alkali cewa yana ganin wasu shige da fice a cikin kotun Wanda baiyarda dashi ba. Anan ne alkalin ya umurci jami’an tsaron farin kaya DSS dasu gudanar masa da bincike na gaggawa a ciki da wajen kotun, kuma nan take suka dawo cikin kotun suka ba alkalin ruhoton cewa tabbas wasu matasa da muggan makamai sunyiwa kotun kawanya amma sun dauki matakin korarsu daga harabar kotun, Alkalin yace su tabbatar babu wata Matsala domin duk abinda yafaru akansu laifin zai kare, suka bada tabbacin sun kore su kuma kowa zai iya fita babu damuwa.
Duk da haka da Mr LA yazo fita kotun saida magoya bayanshi suka rakashi mota amma wasu daga cikin bata garin Matasan da ake zargi wasu ne suka turo su kotun sunyi lanbo wasu kuma daman suna cikin kotun a lokacin inda sukayi kokarin kaiwa Mr LA hari amma basuyi nasara ba.
Mr LA yace rayuwar sa na cikin hatsari kuma ya roki a bashi jami’an tsaro domin kula dashi saboda barazanar da yake fuskanta a wannan shari’ar Lawal Adamu Usman…..

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *