CUTAR COVID-19 KIMANIN MUTUM 616 SUKA SAKE MUTUWA A BIRTANIYA
Jumillar mutum 18,738 ne suka mutu a asibitocin Birtaniya sakamakon annobar cutar korona ya zuwa karfe 5:00 na yammacin Laraba, a cewar Sashen Lafiya na kasar.
Adadin ya kai haka ne bayan an samu karin mutum 616 da suka mutu a rana kafin wancan.
Sai dai adadin bai hadar da na wadanda suka mutu a unguwanni da gidajen gajiyayyu ba.