SAMUWAR KORONA BAIROS YA KARA YA WAN MATALAUTA A DUNIYA

SAMUWAR KORONA BAIROS YA KARA YA WAN MATALAUTA A DUNIYA

Inji Antonio

Daga Zubairu M Lawal

Babban Sakataren Majalisar DInkin Duniya Mista Anotonio Guterres ya bayyana haka a wata wasakar da ya aika  na nuna damuwa ga yadda tattalin arziki kasa shen Duniya ya tabarbare.

Babban Sakataren ya qara da cewa hanyoyin samun kudaden shiga  da ake amfani da su a baya duk sun tsaya yanzu saboda samuwar Wanan cutar.

Ya ce  yanzu an kara samu ya wan matalauta saboda cutar ta talautar da miliyoyim al’umma a duniya.

Da yawan yan kasuwa harkoki sun tsaya saboda kulle da akayi wa al’umma a gidaje . Kamfanoni da hanyoyin shiga da fice da ke kawo kudade ko mai ya tsaya .

Babban sakataren ya ce ya kamata qasa shen Duniya su canja salon samar da hanyoyin samun kudin shiga a wannan yanayi da ake ciki na cutar Korona bairos.

Sakataren Majalisar Dinkin Duniya ta ya yi kira akan qasa shen Duniya da su canja salo su kirkiro wasu hanyoyi wadanda za su farfado da tattalin arziki da kuma samar da aikin yi masu yawa a tsakanin Al’umma

Ya qara da cewa  tunda ake a tarihi ba’a taba ganin cuta irin wannan ba, wacce ta sa arzakin Duniya ya girgiza, aka rasa aikin yi a gaba dayan Duniya.

Ya ce yanzu halin da ake ciki talakawa sun kara yawa acikin Al’umma a fadin Duniya, dan haka mutane na cikin wahala musammamma mata da kanan yara.

Ya ce , yanzu Duniya ta shiga halin kunchi na rashin walwala yara suna killace a gida an rufe dukkan makarantu .

Ayyukan cigaba da Majalisar Dinkin Duniya ke yi a qasashen duniya komai ya yi baya saboda halin kunchi da cutar Korona bairos ta sanya Duniya a ciki.

Ya bukaci iyayen yara da su kulla da rayuwar yara masamman qananan yara dake cikin kuruciya . kuma kungiyoyin mata masu fada aji su shelanta yaki da cutar Korona bairos da gangamin wayar da kan alumman karkara.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *