MURNAR BIKIN CIKA SHEKARA GUDA A KAN MULKI GWAMNA ABDULLAH SULE YA ZIYARCI AL-MAKURA
Daga Zubairu M Lawal
Gwamnan jihar Nasarawa Injiniya Abdullah Sule ya ziyarci tsohon Gwamnan jihar kuma Sanata mai ci a mazaber Nasarawa ta kudu.
Bayan kammala shagulgular murnar bikin cika shekara guda bisa kan karagar mulki jihar Nasarawa Gwamna Abdullah Sule yayi tattaki zuwa birnin tarayya Abuja zuwa gidan tsohon Gwamna Umar Tanko Al-makura.
Cikin kasidar da yarabawa manema labarai mai taimakawa Gwamnan kan harkokin manema labarai Malam Yakubu Lamai ya ce, Gwamna Abdullah Sule ya ziyarci Sanatan ne da zimmar taya shi murnar cika shekara guda bisa kujerar Sanata a Majalisar Dattijai ta kasa.
Sannan ya yabawa Tsohon Gwamnan saboda yadda har yanzu bai hutaba yake hidima ga alumman mazaver shi.
Gwamnan Abdullah Sule ya ce, muna ganin kyawawar jagoranci daga Sanata Umar Tanko Al-makura. Sannan zamu bi tsare tsaren shi wanda ya bi wajen ciyar da jihar Nasarawa zuwa ga tudun mun tsira.
Gwamna Abdullah Sule ya jinjina wa Al-makura yadda ya yi gwagwarmayar tabbatar da zaman lafiya a ciki da wajen jihar Nasarawa. Ya ce , yau kwana 365 ke nan muma muke bisa kan wannan kujerar Kuma muna amfana da shawarwarin dattawan jihar Nasarawa.