Sama da yara 115,800 akayiwa gwajin Annobar Korona a Nijeriya
UNICEF
Daga Zubairu M Lawal
Hukumar kula da qananan yara ta Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ta ce Gwamnatin tarayyar Nijeriya tayiwa yara qanana gwajin Annobar cutar Korona bairus a lokacin da cutar tayi kamari a Duniya.
Mista. Peter Hawkins Babban Jami’in ne na ya ce UNICEF tabbatar da shedar Gwajin ta takardan shedar da suka shigo hannun Ma’aikatan ta daga cibiyoyi dabam dabam.
Ta ce kimanin yara qanana da yawan su ya kai 115,800 akayiwa gwajin Annobar cutar Korona bairus a jihohin dabam dabam a fadin Nijeriya.
Kuma Shugaban yaki da Annobar cutar Korona bairus ta Nijeriya ya tabbatar da haka ta hanyar rattaba hannu kan kowani takardan sheda.
An kuma gudanar da gwajin ne a cibiyoyin da ake Gwajin kwayar cutar Korona dake wasu jihohin.
UNICEF ta ce gwajin da akayiwa yaran ya taimaka sosai wajen dakile yaduwar annobar cutar Korona bairus a fadin Nijeriya.
Ya qara da cewa babban damuwar UNICEF shine halin da yara qanana zasu tsunce kansu a lokacin cutar Korona bairus da ya addabi al’umman Duniya ciki harda Nijeriya.
Zuwa hutun dole na rufe makarantu da zaman gida ya taimaka wajen dakile yaduwar annobar cutar a cikin jama’a saboda yara qanana suna hulda da kowani irin mutani.