A daren jiya – YAN BINDIGA SUNYI GARKUWA DA SHUGABAN JAM’IYYAR APC TA JIHAR NASARAWA

Yan Bindiga sunyi Garkuwa da Shugaban APC ta jihar Nasarawa

Daga Zubairu M Lawal Lafia

A ranar Asabar da misalin karfe goma shadaya saura mahara da ba a tantance ko suwa ye ba sukayi Garkuwa da Shugaban Jim’iyyar APC ta jihar Nasarawa Mista Philip Tatari Shekwor.

Lamarin ya sanya dubban jama’a mazauna unguwar cikin fargaba.
Inda suka rikajin karar Harbe-harbe Bindigogi a unguwar cikin dare. Mista Philip Shekwor yana zaune ne a unguwar Kurukyo cikin garin Lafia.

Kwamishinan yan sandan jihar Nasarawa Mista Bola Longe ya tabbatarwa manema labarai faruwan lamarin.

Ya kuma ce ya zuwa yanzu Rundunar yan sandan jihar Nasarawa sun baza komarsu ko ta ina domin ganin a samo inda aka boyeshi sannan a dawo da shi cikin iyalansa lafiya lau a kuma kama wadannan miyagun.

Ya zuwa lokacin hada wannan Rohotu babu wani magana mai karfi da aka ji daga wadanda sukayi Garkuwa da Shugaban APC.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *