MASU GARKUWA DA MUTANI SUN SACE MUTUM 20 SUN KA SHE DAYA A NASARAWA
Gungun yan Ta’adda dake dauke da miyagun makamai sun addabi al’umman a yan kin Karamar Hukumar Toto dake jihar Nasarawa sun kashe mutum daya sun kumayi Garkuwa da mutum 20.
Mutanin da yan Ta’addan suka far masu matafiyane wadanda ke kan hanyar zuwa Nasarawa dsgaToto. yan Ta’addan sun tsare hanyar Buga-Gwari da ya hada Gadabuke a kan hanayr Toto.
Lamarin ya faru ne a daren Littinin misalin 6:30pm zuwa 7:pm yan ta’addan sunyi ta harbi kan mai uwa da wabi idan nan take suka tsai da duk wani mota dake zuwa.
Sun kuma tafi da mutanin da suka sace a nan ne suka kashe mutum daya mai suna Malam Silihu suka jefar da gawar.
Rundunar yan sandan jihar Nasarawa ta tabbatar da faruwan lamarin a ta bakin jami’in hulda da jama’a na Rundunar Mista Ramham Nelson ya sheda wa manema labarai cewa abin ya farune a cikin daren Kuma Rundunar yan Sanda sun kai dauki amma sun tarar da mota daya ne mai lamba NTT 265 AA.
Amma basu da labarin adadin mutanin da aka sace. Kwamishinan yan Sandan jihar Nasarawa Bola Longe ya ummurci DPO da ya dauki motar da a ka gani a wajen zuwa ofishin yan Sanda dake Toto.
Shugaban karamar Hukumar Toto Hon.Nuhu Adamu Dauda ya sheda faruwan lamarin. Idan ya tabbatar da cewa an sanar da shi cewa yan Bindiga sun kashe mutum daya kuma sun yi Garkuwa da wasu .
Ya ce mun tura Rundunar yan Sintiri sun shiga dajin inda suka tarar da gawan wani mutum daya a kusa da kauyen Gubasa.
Sun daukoshi an tabbatar da wadanda suka sanshi Malamin Makaranta ne a yanzu, a baya jami’in Hukumar zave ne a jihar Nasarawa.
Shugaban karamar Hukumar ya ce har yanzu yan sintirin suna daji suna bincikawa ko Allah zai sa a gano mutanin da Kuma mabuyar yan Ta’addan.
Sannan yayi kira ga al’umman yankin Toto dasu rika bayyanawa jami’an tsaro duk Wanda suka san yana aikata ire-iren wannan aiki ko makqmancin sa, ko kuma wanda suka gani basu amince da take taken sa ba.
MDD ta yaba da yadda kiristoci su ka gudanar da bukin Kirsimeti cikin kariyar Korona
Daga Zubairu M Lawal Lafia
Babban kodineta a ofishin Majalisar Dinkin Duniya dake Nijeriya Mista Edward Kallon ya yabawa mabiya addinin kirista dake tarayyar Nijeriya kan yadda suka kiyaya dokokin Korona a bukin Kirsimeti da sabuwar shekara.
Ya ce duk da cewa babu dadi ace mutani sun gudanar da shagulgula a irin wadannan ranakun cikin takura. Amma Majalisar Dinkin Duniya tayi farin ciki da bin wannan dokar da Hukumar Lafiya ta Duniya ta fitar wato(WHO), dan gane da yadda annobar cutar Korona bairus ke yaduwa kamar wutan daji.
Ya qara da cewa hukumar binciken cututtuka (NCDC) ta bayyana yadda cutar Korona ke kara yaduwa a Nijeriya ta kuma bayyana dokokin da ya kamata a dauka a lokacin shagulgular bukin ranar Kirsimeti.
Tun daga ranakum 25 ga watan Dasambar zuwa daya ga watan janairu ta shekarar 2021.
Mista Edward Kallon yace ba a samu cin koso a guraren Majami’u ba kuma da dama sun gudanar da ibadun su a kebe ba tare da tara cin koson mutani ba.
Ya ce wannan sakon na kiyaye taron cinkoso a guraren ibada na bukukuwan Kirsimeti da sabon shekara da aka rika yayatawa a kafafen yada labarai da kafafen sada zumunta yayi amfani so sai.
Rigakafin cutar Korona yana da mahimmanci ga al’umman Nijeriya
Inji MDD
Daga Zubairu M Lawal Lafia
Babban mai ba da shawara a ofishin Majalisar Xinkin Duniya da ke Nijeriya mista Martin Ejidike, ya bayyana haka.
Ya bayyana mahimmanci yin aluran Rigakafin annobar cutar Korona saboda Rigakafin yafi mahimmanci kan cewa sai mutum ya kamu da cutar sannan ya bukaci magani.
Kiyaye Dokokin yaduwar cutar yana da mahimmanci saboda zaiyi ta siri a cikin al’umma.
Kiyaye dokokin da suka hada da wanke hannaye da safa man hanyaye da rufe fuska suna da mahimmanci saboda suna bada kari ga wanda yake dauki da cutar ko Wanda baya dauke da cutar.
Duk Wanda yake dauke da cutar Korona bairus idan yana amfani da takunkumin rufe fuska da hanci da baki koda yayi atishawa ko tari ba zai yi tasiri akan wanda yake nesa da shi ba.
Saboda akwai kariya daga wannan takunkumin da yake sanye da ita. Wanke hannaye yana rage karfin cutar ga wanda yake dauke da ita koda ya rungume mutum saboda yana wanke hannaye kuma akwai man sinadari na kariya a jikin sa.
Amma mafi alheri bada tazara da rashin shan hannaye yafi komai mahimmanci daga cikin Dokokin kariyer yaduwar annobar cutar.
Yin aluran Rigakafin zai taimaki al’umman qasa wajen yakar yaduwar cutar a fadin qasa cikin al’umma.
Cibiyar yada labarai na ofishin Majalisar Xinkin Duniya dake Nijeriya ta dukufa wajen kara wayar da kan al’umma game da mahimmanci yin aluran Rigakafin.
Mista Martin Ejidike ya ce idan kashi 70 cikij 100 zasu yi aluran Rigakafin kariyar annobar cutar Korona bairus to za a samu dauki daga yaduwar cutar a Nijeriya.