ABIN TAUSAYI – AN SAKO DALUBAN ISLAMIYYA DA SUKA KWASHE KWANAKI 88 A HANNUN MASU GARKUWA DA MUTANI.

KOMAI NISAN JIFA – AN SAKO DALUBAN ISLAMIYYA DA SUKA KWASHE KWANAKI 88 A HANNUN MASU GARKUWA DA MUTANI.

Sama da dalibai 70 na makarantar Islamiyya da ke garin Tegina wadanda ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su a jihar Neja, masu garkuwa da mutane sun sako su.

Jaridar Duniyarmu Ayau, ta ruwaito, an sace Daliban ne daga harabar makarantarsu tun a watan Yuni.

Wata majiyar tsaro ta shaida wa PRNigeria cewa daliban na kan hanyarsu ta zuwa Minna akan hanyar Kagara daga Birnin Gwari.

Rahotanni sun nuna Daliban Islamiyyar sun kwashe tsawon kwanaki 88 a hannun masu garkuwar .

PRNigeria tana wallafa adadi tun bayan sace daliban a Arewacin Najeriya. Daliban da aka sace na Kwalejin Gwamnatin Tarayya ta Yauri Suma sun kasance a tsare na tsawon kwanaki 70 yayin da sauran daliban da aka sace na wata Makarantar Baptist a Kaduna suka shafe kwanaki 52 a hannun masu garkuwa da mutane.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *