Sarkin Musulmi ya jaddada kudurin tabbatar da zaman lafiya a Nijeriya
Daga Zubairu .Lawal
Sarkin Musulmin Nijeriya Alhaji Sa’ad Abubakar ya jaddada kudurinsa na tabbatar da zaman lafiya a tarayyar Nijeriya. Ya Kuma yabawa Sarakunan Gargajiya na Nijeriya saboda yadda suke bada gudumawa sosai wajen tabbatar da zaman lafiya.
Da yake jawabi a taron Sarakuna da masu ruwa da tsaki wanda Majalisar Dinkin Duniya ta shirya tare da hadin giwar kungiyoyin agaji masu zaman Kansu.
Taron ya hada Sarakunan Gargajiya na Arewaci da Malaman Addinai da Shugabannin kungiyoyi.
Yace; Sarakuna suna kusa da jama’a Kuma suna lura da yadda al’umomi Ke gudanar da ayyukan zaman takewa a tsakaninsu.
Bil hasali Sarakunan Gargajiya na sanya ido da duba rayuawar jama’a da tattauna lamurar zaman takewa da baiwa jama’a shawarwari na zaman lafiya da hadin kai a tsakaninsu.
Sanan yayi kira ga Gwamnatoci da su rika hadin kai da Sarakuna wajen tabbatar da cigaban al’umma domin karfafa zaman lafiya.
Shima Shugaban Kungiyar Kiristocin Nijeriya Rev. Samson Ayokunle,ya yabada kalaman Sarkin Musulmai na cewa ya kamata al’umman Nijeriya su zaman tsintsiya madaurinki guda, su kuma fahinci juna su zauna lafiya.
A jawabinta Mataimakiyar Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Hajiya Amina Muhammad ta yi kira ga Gwamnatoci da Sarakunan Gargajiya dasu rika daukar mataki na yaki da cinzarafin mata da yara kanana.
Tace; ya kamata a daina tura yara qanana aikin aikatau saboda yana janyo damuwa wasu yaran ta nanane suke fadawa halin kunci.
Ministan Harkokin Mata Misis Dame Pauline Tallen, ta yabawa Sarakunan Gargajiya kan yadda suka taka rawa wajen fadakar da al’umma mahimmanci kiwon lafiya a lokacin Korona.
Ta rokesu dasu cigaba da baiwa yaki da cin zarafin mata da yara kanana goyon baya.