Yadda matan karkara zasu amfana da tallafin Sana’a a Sokoto
Inji Edward Kalon
Daga Zubairu Lawal
Mista Edward Kalon shine Babban jami’i a ofishin Majalisar Xinkin Duniya dake Nijeriya ya bayyana shirin da sukayi na kai dukin tallafi ga matayen dake rayuwa cikin kunci a wasu sasa na jihar Sokoto.
Yace; an cimma yarjejeniya tsakanin Gwamnatin Jihar Sokoto da Majalisar Dinkin Duniya da Gwamnatin tarayya kan hanyoyin da za a ka tallafin na musamman na cigaban matayen karkara.
Mista Edward Kalon yace ; kimanin mataye dake rayuwa cikin kunci sama da 6000 ne zasu amfana da wannan sabon tsarin na sauyin yanayi.
Matayen da suka fito daga kauyen Wamako da Bodinga, da kuma Wurno. Yace ; a gewayen da kwamitin tallafin tayi ta zakulo matayen dake rayuwa cikin kunci da yara kanana da iyayensu suka mutu suka barsu.
Sanan iyayen mata basu da karfin daukar dawainiyan karatun yaran da biya masu bukatu na yau da kullan.
Za a koyar da matayen sauyin sana’o’i dabam dabam a kuma koyar dasu huldar kasuwanci a basu yan kudaden da zasu jali domin taimakon kawunasu.
Yace ; duk da cewa wannan yana daya daga cikin kuddurorin Gwamnatin jihar Sokoto amma samun hadinkan Majalisar Dinkin Duniya da Gwamnatin tarayya zai kara masu karfi