Za tabbatar da zaman lafiyan Nijeriya idan na zama Shugaban kasa Inji Bokola Saraki

Za tabbatar da zaman lafiyan Nijeriya idan na zama Shugaban kasa

Inji Bokola Saraki

Daga Zubairu M Lawal

Dan takarar kujerar Shugabancin Nijeriya a Jam’iyyar PDP Sanata Abubakar Bolola Saraki ya bayyana cewa “zai tabbatar da zaman lafiya a Nijeriya”.
Dan takarar ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da Membobin Jam’iyyar PDP ta jihar Nasarawa.

Saraki yace; yanzu al’umman Nijeriya sun cikin tsaka mai wuya matsaloli sunyi yawa ga rashin tsaro ga yunwa Babban matsalar tabarbarewar tattalin arziki Nijeriya.

Sarki yayi alkawarin idan PDP ta tatsai da shi takarar Shugabancin Nijeriya, kuma yayi nasara a zaben 2023 zai inganta tattalin arziki ta yadda al’umman Nijeriya zasu amfana.

Kuma zaiyi amfani da Na’urarori wajen magance matsalar tsaro ta yadda za’a gane beta gari ba tare da beta lokaci ba.

Yace Gwamnatin APC ta wargaza komai matsaloli sunyiwa Nijeriya yawa babu zaman lafiya kasar kamar babu Gwamnati.

Ya qara da cewa akwai jihohi da dama da suke da albarkatun kasa na noma, ciki harda jihar Nasarawa zai farfado da harkan noma ta yadda zai kore yunwa da tsadar rayuwa.

Al’umman Nijeriya suna bukatar jajirtacen Shugaba daga PDP kamana wanda yasan mulki ya iya gudanar da mulki wanda zai jagorancin gyara kasan nan.

A nasa jawabin Shugaban jam’iyyar PDP ta jihar Nasarawa Hon.Frances Orogu yayi kira ga matasa maza da mata dasubaiwa Jam’iyyar PDP kuri’unsu domin ceto Nijeriya daga matsalolin da Gwamnatin APC ta jefa kasar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *