Rikici ya barke wajen gudanar da zaben fidda gwani a mazaber shugaban Jam’iyyar APC ta kasa a Nasarawa

Rikici ya barke wajen gudanar da zaben fidda gwani a mazaber shugaban Jam’iyyar APC ta kasa a Nasarawa

Daga Zubairu M Lawal

Cikin daren yau Lahadi misalin 10 pm rikici ya barke wajen gudanar da zaben fidda gwani na Jam’iyyar APC a mazaber shugaban jam’iyyar APC ta kasa.

Lamarin ya farune cikin  harabar Jami’an jihar Nasarawa dake garin Keffi.

Da yake zantawa da manema Labarai daya daga yan takarar kujerar Sanata Barrister Labaran Shuaibu Magaji (Matawallen Toto) yace; da yammacin yau ne aka kirashi akace ga Malaman zabe da masu kada kuri’a sun iso harabar da za a gudanar da zaben.

Yace; nan take ya isa garin tun daga kofar shiga ya tarar da motoci da jama’a sunyi dogon layi ana tantancesu.

Ya karasa gurin zaben ya tarar da malamin zaben yana jawabi ga Hukumomi tsaro yadda za’a gudanar da zaben.

Nan take ya gabatar da kanshi a matsayin Dan takarar da za a gudanar da zaben da shi. Sannan ya tambayi Malamin zaben cewa ina masu kada kuri’ar suke?.

Malamin zaben yace gashu a kofar shigowa cikin jami’ar.

Barrister yace Kananan Hukumomi nawa?

Malamin zaben yace biyar.

Barrister banga yan Karamar hukumar Toto da Nasarawa ba?

Malamin zaben suna cikinsu.

Barrister yace; nan take na kira Gwamnan jihar Nasarawa Injiniya Abdullah Sule na sanar dashi halin da ake cikin.

Sai Gwamna Abdullah Sule yace;  yanzu haka yana tare da Shugaban Jam’iyyar APC ta jihar Nasarawa tare da Sakatarensa.

Nan take Shugaban Jam’iyyar APC ta jihar yace ai masu zaben fidda gwani na Sanata suna nan a cikin garin Lafia suna gudanar da zaben Dan takarar kujerar Majalisar Wakilai na mazaber Nasarawa da Toto wanda aka samu sabani  jiya gurin zaben a Nasarawa.

Malamin zaben yaji haka amma yace; shifa wadanda aka bashi su Ke nan.

Barrister Magaji yace; bai yarda da wadannan mutaninba.

“Nasan muna da masu kada kuri’a kimanin mutum 135 suna Lafia Dan haka naki amincewa da wadannan masu zaben na boge da aka kawo”.

Nan dai malamin zaben yace san shi da wadannan zaiyi zabe.

“Nace to a tsarin zaben Shugaban jam’iyya na Karamar hukumar zai tabbatar da wannan daga yankinsa ne, sannan akwai nuna katin Jam’iyya, ko katin Dan kasa ko amfani da layin waya.

Saboda haka za ayi amfani da takardan sunayen masu zaben a tabbatar da ko sune.

Malamin zaben yaki amincewa,

Daga bisani an bukaci muzauna a tattauna.

Ni Labaran Magaji da Arc.Shehu Tukur da Malamin zaben.

Munyi ta tattaunawa an kasa fahintar juna nace yanzu darene a daga zaben zuwa gabe karfe 10am ido na ganin ido zai fimana sauki saboda kowa ya huta”.

Wakilinmu dake wajen zaben ya tabbatar Kafin a kai ga bayyanawa rikici ya barke tsakanin magoya bayan yan takarar biyu inda takai ga haurowa zuwa filin zaben.

Jami’an tsaro sunyi amfani da hayaki mai sa hawaye wajen tarwatsa gungun matasa masu rikicin.

Barrister Labaran Shuaibu Magaji yace yana nan daran a Jam’iyyar APC kuma yana cikin jerin yan takarar kujerar Sanata a mazaber Nasarawa ta yamma bai hakura ba aje ayi zaben gaskiya Wanda Allah ya bashi nasara a rufa masa baya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *