KU KARANTA – Gwamna Abdullahi sule ya amince da daukar sabbin Malamai a jihar Nasarawa

Gwamnatin jihar Nasarawa ta amince da daukar Malamai 550

Daga Zubairu M Lawal

Gwamnan jihar Nasarawa Injiniya Abdullah Sule ya amince da daukar sabbin Malamai da yawansu ya kai 550 a fadin jihar.

Gwamnan ya bayyana hakane wajen taron karawa juna sani na Shugabannin Makarantun Sakondire na tsawon kwanaki uku, dake gudana a GSSS dake garin Lafia.

Gwamnan yace; Babban muradin Gwamnatinsa shine ganin cewa daluban jihar sun samu ilumi mai inganci.

Taron da ya samu halartan Shugabannin Makarantun Sakondire na Gwamnati da masu zaman kansu da adadinsu yakai 250.

Gwamnan ya janyo hankalin Shugabannin Makarantun wajen samar da manhajan ilumin bai daya da zai inganta karatun yara.

Gwamnan Sule Shugabannin dasu tabbatar suna amfani da kwararun Malamai masamman a fannim ilumin kimiyya da fasaha.

Ilumin kimiyya da fasaha yana tasiri wajen gina kasa da tattalin arzikin kasar.

Gwamnan yace; wannan bitar zai dauki sabon shafi wajen fahintar juna.

Ya qara da cewa Gwamnatin jihar tana kokari wajen ingatan ilumi saboda tana kula da gyaran makarantu da samar da kayyakin karatu ga dalubai a fadin jihar Nasarawa.

Itama a nata jawabin Kwamishiniyar Ilumi na jihar Nasarawa Hajiya Fati Jimita tace makasudin wannan taron karawa juna sani ga Shugabannin Makarantun Sakondire shine farfado da darajar ilumin bai daya.

Tace; ire iren wannan taron yana kara samar da fahintar juna. kuma tana da yakinin taron zai haifar da da mai Ido a jihar.

Tace; a wannan taron wani zai amfana da fahintar wani. Haka zalika Makarantu masu zan kansu da makarantun Gwamnati zasu samu tsari guda ta yadda daluban jihar zasuci gajiyar Ilumi mai inganci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *