Wata amarya ta tsinci kanta a gidan yari bayan da ta sumar da kishiyarta sakamakon ribibin shiga gidan gaba a motar mijinsu.Jaridar Daily Nigerian ta ba da rahoton cewa lamarin ya faru ne a Jihar Kano a makon da ya gabata, bayan da uwargidan ta shaida wa Babbar Kotun Shari’ar Muslunci da ke Kofar Kudu ƙarƙashin Mai Shari’a Ibrahim Sarki Yola, inda ta yi ƙorafin cewa kishiyarta ta mata duka.

A cewar mai ƙarar, ba ta da lafiya, sai mijin nasu ya aiko da mota a kai ta asibiti, sakamakon ita ba za ta iya tuƙa tata motar ba.

Ta ƙara da cewa shigar ta motar ke da wuya, kwatsam sai ta ga kishiyarta riƙe kofar motar tana ce mata ta fito, sai ita kuma uwargidan ta ce mata ba za ta fito ba saboda asibiti za a kai ta.

“Kafin ka ce kwabo, sai na ji ta doke ni a goshi na. Nan na faɗi a sume, shi ne aka garzaya da ni asibiti,” in ji uwargida.

Sai dai kuma amaryar ta musanta laifin da ake zarginta da aikatawa.

Daga nan ne Mai Shari’a Sarki Yola ya sa aka aike da Amaryar gidan yari zuwa mako mai zuwa domin ci gaba da shari’ar.