AN FARA – Wane Hali ‘Yan Arewa 298 Da Amotekun Ta Kama Ke Ciki?

AN FARA – Wane Hali ‘Yan Arewa 298 Da Amotekun Ta Kama Ke Ciki?

Kwana uku bayan rundunar tsaro a Kudu maso Yamma ta Amotekun ta kama ’yan Arewa 147 a Jihar Oyo, ita ma takwararta ta Jihar Ondo ta yi irin wannan kamun na mutum 151.
An kama matafiyan ne a Akure, babban birnin jihar a ranar Juma’a a cikin wata motar tirela da ta taso daga Arewa zuwa Kudu maso Yammacin Nijeriya.
Ana zargin su da cewa ‘yan ta’adda ne da ke neman yin kutse da kuma samun mafaka a shiyyar kudu maso yammacin Nijeriya.
To sai dai mutanen na cewa su ‘yan ci-rani ne da kan shiga kudancin kasar domin neman na halaliya.
Da yake tabbatar da kamen, Shugaban kungiyar Fulani makiyaya ta Miyetti-Allah reshen jihar ya Ondo, Alhaji Bello Garba ya shaida wa Aminiya cewa, “Gaskiya ne a ranar Juma’a da safe jami’an Amotekun sun tsare wata motar tirela da aka yi bincike aka gano tana dauke da mutane 127 da buhunan shinkafa da wake da babura guda 10.
“Rundunar ta bayar da umarnin tsare mutanen da suka mallaki wadannan babura guda 10 ne saboda bincike ya tabbatar da baburan ba su da takardu.
“Amma an sallami sauran mutanen saboda ba a gano haramtattun abubuwa ko makamai a tare da su ba.
“Rundunar ce ta gayyace ni zuwa wajen binciken da na tsaya da kaina domin ganin an yi masu cikakkun takardu zuwa yammacin wannan rana da aka sallame su,” in ji shi.
Sai dai da yake yi wa ’yan jarida cikakken bayani, Kwamandan Rundunar Amotekun ta Jihar Ondo, Akogun Adetunji Adeleye, ya ce sun tsare motar ce daga ci gaba da tafiyar domin yin cikakken bincike a kansu.
Mutanen 151, kamar yadda kwamandan rundunar ta Amotekun Adetunji Adeleye ya nuna sun fito ne daga jihohin Katsina da Kano da kuma Jigawa.
Ya ce an kama su da layu da hotuna da ke nuna alamar samun horo na musamman.
Waɗanda ake zargin sun haɗa da wasu mata biyar da suka ɓoye a bayan buhunan wake da shinkafa a cikin tireloli biyu da aka gano a lokacin da jami’an Amotekun suka tsananta bincike.
Adetunji Adeleye ya bayyana cewa an kama manyan motocin da suka yi jigilar mutanen ne biyo bayan rahoton sirri da suka samu.
Ya ce, an tare motocin ne a kusa da hanyar Sango da Akure zuwa Ado, bayan da jami’an kungiyar sintirin suka fara zargin abubuwan da suke dauke da su cikin manyan motocin inda suka gano mutane cunkushe a ciki.
Ya ce, “Mun kama wasu manyan motoci guda biyu dauke da mutane 151 da suka yi dubara suka boye a bayan buhunan shinkafa da wake, ta yadda ba za a iya sanin adadin mutanen da ke a cikin motocin ba.
“Bayan an kama su, mun yi masu tambayoyi, wasu sun ce za su je Akure a jihar Ondon, yayin da wasu suka ce Osogbo a jihar Osun.
“Ko da yake, ba mu kammala daukan bayanansu ba, domin babu wani daga cikinsu da ya san abin da zai je yi ko kuma aikin da zai yi.
“Abin da suka iya gaya mana shi ne, sun shiga motar ce suka zo Jihar Ondo,”in ji Mista Adeleye.
Shugaban na Amotekun ya ce, “Ka san duk matafiyi akwai nufinsa na inda zai je da abun da zai yi amma sai cewa suke yi za mu je Akure a nan Jihar Ondo da Osogbo a Jihar Osun ne.
“Wannan bai dace ba amma saboda ’yancin kasancewarsu ’yan kasar Najeriya muka kyale su domin babu wani haramtaccen abu ko makami da aka samu a tare da su

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *