Gwamnatin Nasarawa zata dauki mataki kan zubda Bola a magudanan ruwa
Daga Zubairu Lawal
Gwamnatin Nasarawa zata dauki mataki kan masu zuba shara a magudanar ruwa.
Kwamishinan tsaftar muhali ta jihar Hon.Kwanta Yakuba ya bayyana a lokacin da yake zantawa da manema Labarai bayan kammaka dokar shara na karshen wata da Gwamnatin jihar ta tsara.
Kwamisinan yace; Gwamnatin jihar bazata zura ido ta kyale masu zubar da shara a Magudanan ruwa da yake toshe banyan ruwa ya kuma haifar da ambaliyan ruwa a gariba.
Yace; zuba shara a kwalbati magudanan ruwa yana haifar da ambaliyan ruwa, Wanda ke sanya ruwa ke shiga gidajen al’umma.
Kwamishinan yace; dokar da Gwamnatin jihar Nasarawa ta tsara kan tsaftar muhalli yana samun karbuwa cikin fadin jihar.
Yace; duk da ana kama masu kunnin kashi amma yanzu dadama mutani suna kiyayewa suna zama a gidajensu suna tsaftace gidajensu.
Kwamishinan Kwanta Yakubu ya yqbawa Sarkin Lafia mai shari’a Sidi Bage danane da goyon baya da yakeba wannan kuddurin na tabbatar da jama’a sun tsaftace gidajensu.