Zaben Jihar Adamawa anyi nasara da tazarar kuri’u 31,249, an kasa bayyana sakamako
Duk da sakamakon zaben da jam’iyyar PDP ta samu 421524 itama jam’iyya adawa ta APC ta samu 390,275. rHukumar Zabe ta kasa INEC ta ce Akwai Kura a Zaben Adamawa, ya Zama ‘Inconclusive’ INEC a jihar Adamawa ta bayyana rashin amincewa da sakamakon zaben da aka tattara a jihar. inda tace an samu kuskuren da dole a warware kafin ayyana mai nasara a zaben. Hukumar ta bayyana hakan ne a birnin Yola a cibiyar tattara sakamakon zaben da daren Litinin 20 ga watan Maris. Ta bayanin cewa, an soke zabe a mazabu 47 mai adadin kuri’u 41,796, wanda ya zarce adadin kuri’u 31,249 da jam’iyyun PDP tayi nasara dashi. Zaben da ya gudana yar Takarar Jam’iyyar APC Hajiya Aisha Binani ta samu kur’u 390,275 yayin da Gwamna mai ci, Alhaji Ahmadu Finitiri ya samu kuri’u 421,524 a Dan Takarar na Jam’iyyar PDP shine kan gaba da tazarar Kuri’u 31,249