Shugaban hukumar zabe ya gaggauta sauka daga kujerarsa
– Masu sa ido kan zaben Nijeriya
Daga Madina Ibrahim
Hadakar kungiyoyi masu sa’ido kan yadda hukumar zabe INEC ta gudanar da zabukan kasa a 2023, (Coallition of INEC Accredited Domestic Election Observers),
sun bukaci kwamishinan hukumar zabe ta INEC reshen jihar Adamawa Barista Hudu Yunusa, da ya sauka daga shugabancin hukumar.
Kwamared Friday Maduka, mambe a kungiyar ya bayyana haka ga manema labarai a garin Yola jihar Adamawa yace “muna kira ga Kwamishinan hukumar zabe INEC da ya sauka daga shugabancin hukumar kafin lokacin da za’a kammala zaben Gwamna a jihar, muddin ba zai iya ba.
“Idan ya tabbatar ba zai iya gudanar da zaben ba, ya sauka daga shugabancin hukumar, domin jama’an da muka tattauna dasu, sun nuna damuwa kan shugabancinsa, ya sauka domin ayi zaben da zai gamsar da al’umman jihar.
“Mu kasance masu sa’ido domin tabbatar da ganin zaben da za’a sake anyi gaskiya da adalci ga kowa, duk wanda yaci a bashi, muna da mambobinmu duk wuraren da za’ayi zaben” inji Friday.