Zamu cigaba da bunkasa jihar Nasarawa a matakin zaman lafiya – Gwamna Sule

Zamu cigaba da tabbatar da zaman lafiya da hadin kan al’umman Nasarawa
Gwamna Sule
Daga Zubairu .Lawal
Zamu fara daga inda muka tsaya har sai mun zama tankar uwa daya uba daya  cikin jihar Nasarawa. Gwamna Abdullahi Sule yace; mun samu nasarar tabbatar da zaman lafiya da hadin kan al’umman jihar.
Mun magance matsalar mahara masu cutar da jama’a, masamman yan kungiyar Ansarul da makamantarsu.matsalar rigingimun manoma da makiyaya dul ya kau Zaman lafiya mai dorewa ta tabbata daga lokacin da muka fara mulki.
Matsalar albashin Ma’aikata da fansho mun maganceshi. Mun dibe sabbin ma’aikata masamman fannin malaman makarantu.

Mun samar da hanyoyi lungu da sako a guraren da suka cancanta a manyan biranai da karkara.mun samar  da tasoshin mota na zamani a garin Lafia da Karu.

Mun gina kasuwannin zamani garin Keffi Akwanga Nasarawan Eggon. Kudaden shiga da muke samu a jihar muna aiki dashine saboda bunqasa jihar.
Mun taimaka wajen bada tallafin kiwon lafiya. AkwI dubban mata da muke basu tallafin 5000 a dukkan Qananan hukumomin jihar.
Zamu cigaba da ayyukan raya biranai da karkara a fadin jihar. Mun  aza tubalin gina sabon sakatariyar Ma’aikata na jihar
Harkan Noma da kiwo ba a barsu a baya ba.zamu kara fadada hanyoyin samun kudaden shiga. Sabon tashar jirgin samanmu Gwamnatin tarayya ta karba, za a kara gyaranshi. Gandun dajin farin ruwa shima ya koma mallakin Gwamnatin tarayya.
Yanzu jihar Nasarawa ta kasance cikin jerin jihohin da suke da arzikin manpetur da sauran ma’adinai. Idan mukaci gaba da bunqasa harkan Noma jiharmu zatayi fice wajen samar da abinci mai yawa da inganci a qasarmu.
Jihar Nasarawa ta amfana da Gwamnatin Muhammad Buhari. A lokacin Gwamnatin Muhammad Buhari an gina cibiyar hurar da Jami’an tsaro na qasa  cikin jihar Nasarawa.
An kammala gina gadar Loko da ta hada da jihar  Benue.
Yanzu siyasa ta kare, ni Gwamnane na kowa da kowa babu bambamcin siyasa ko addini ko kabila mu zama yan jihar Nasarawa uwa daya uba daya. Mu hada karfi da karfe mu gina jihar Nasarawa da arzikin da Allah ya bamu.
Cikin jawabin Gwamna Abdullahi Sule da ya gabatar bayan rantsar da shi bisa kujerar Gwamnan jihar Nasarawa karo na biyu. A filin taro na garin Lafia wannda mai Babban Alkalin jihar Hajiya Aisha Bashir ta jagoranta a ranar Littinin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *