Nasarar Gwamna Abdullahi Sule a Kotun daukaka kara cigaban Jama’an Nasarawa – Piter Ahmba

Nasarar Gwamna Abdullahi Sule a Kotun daukaka kara cigaban Jama’an Nasarawa – Piter Ahmba
Mai baiwa Gwamnan Abdullahi Sule shawara kan harkokin manema Labarai Hon. Piter Ahamba ya bayyana gamsuwar sa da cewa kotun koli zata maimaita hukuncin da kotun daukaka kara tayi ne wacce ta ayyana shi
Hon. Ahamba yace wannan nasarar cigabane ga al’umman jihar Nasarawa ta kowani bangare.
Ahmba Ya shawarci al’umman jihar Nasarawa dasu cigaba da zaman lafiya da hadin kai dan samun cigaba da ayyukan alheri.
Yace; wannan farin cikin ba na jam’iyyar APC kadai bane na al’umman jihar Nasarawa ne baki daya.
Ya bukaci al’umman jihar dasu cigaba da tabbatar da hadin kai da zaman lafiya domin cigaba da gudanar da ayyukan cigaba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *