An sace jaririya a Asibitin Dalhatu Araf Specialist dake Nasarawa
Daga Zubairu Lawal
A ranar Talata da rana tsaka aka saci jaririya sabuwar haihuwa a Babban Aisibitin Dalhatu Araf ( Specialist Hospital) dake garin Lafia.
Lamarin kamar almara yadda aka saci jaririyar ko sama ko kasa a daken jinya dake Asibitin.
Mahaifiyar jaririyar Wosilat Sulaman ta kasance cikin firgici na rashin ganin jaririyar da ta Haifa. Bayan anyi mata tiyata kwana daya. Lokacin da take kwance bisa gadon jinya tare da yar uwanta dake kula da ita.
yar uwan Wosilat Sulaiman dake kula da ita tace ta manta da cajanta a gida, ta ummhrci wata mata da ke zurga zurga a dakin jinya kamar tana jinyar wata ko kawo ziyara, data kula mata da yar uwanta duk abinda takeso ta bata.
Bayan yar uwan Wosilat ta sanar da Wosilat zataje gida ga Wanda zata kula da ke kafin na dawo.
Fitanta ke da wuya matar ta dau jariri dake kwance kusa da Mahaifiyarsa da nufin zataje masa wanka. uwar jaririn ta nuna rashin amincewa da hakan, amma matar tace akwai sauran kayan wankan jarirai a daki na biyu da nake jinya.
Fitanta ke nan Shuru har yanzu babu labarin wadanda suka saci jaririn ko da zimman sata ko Garkuwa da jariri babu amo ba labari.
Duk da cewa wannan shine karo na farko amma hukumar kula da Asibitin ta dauki kwakwarar mataki. Ya zuwa yanzu an kama Ma’aikatan dake kula da dakin sannan an kama yar uwan Wosilat domin gudanar da bincike.