Ambude cibiyar koyawra na hukumar shiga da fice na kan iyakan Nijeriya
Daga Zubairu M.Lawal
A watan da yagabatane hukumar shiga da fice ta Duniya ta jagoranci bude cibiyar koyarda fasaha da iya ayyuka ga hukumar shiga da fice dake tarayyan Nijeriya. An gina wanan katafarin wajen koyarwane a Helkwatar hukumar dake birnin Abuja.
Cibiyar zai rika koyar da ma’aikatan shiga da fice ta hayoyin da zasu }ara kwarewa wajen gano miyagun alumma da ke shiga }asashe ba bias }a’ida ba.
Da yake jawabi a madadin hukumar shiga da fice ta Duniya Mistar Fernando Medina. Yace; wanan cibiyar da aka gina an samar da kwararun kayan aiki na zamani masamman na’u’rori masu }wa}walwa.
Ya kara da cewa yanzu ma’aikatan shiga da fice na Nijeriya zasuga canji wajen aikace aikachensu.
Yace; wanan }arin illumine da koyan makaman aiki. Kuma akwai tsare-tsaren da dama day a zama tamkar makarantar koyon aikin hukumar shiga da fice na kan iyakokin }asashe.
Ya karae da cewa akwai gurare da dama day a kamata a inganta ofisoshin hukumar bayan Abuja da Kalaba akwai iren su Kano Akwa-Ibom Edo Ogun duka cibiyoyine da ma’aikatan kan gudanar da ayyuka sosai sai dai suna bukatar kayayakin zamani na bincike.
Abaya dai an riga samun mutani masu aiakata miyagun laifuka sukan shigo garurun dake kusa da kan iyakokin nijeriya da sunan yan gudun hijira. Hakan yasanya wasu ke shiga da wasu abubuwan da ba’a ganosu akan lokaci sai an hada da Na’urori masu bincike.