AN NUNA DAMUWA DA YADDA CUTAR COVID-19 KE KARA YADUWA A TARAYYAR NIJERIYA

AN NUNA DAMUWA DA YADDA CUTAR COVID-19 KE KARA YADUWA A TARAYYAR NIJERIYA

Daga Zubairu M Lawal

Majalisar Dinkin Duniya da tarayyar Turai sun nuna damuwa kan yadda annobar cutar Korona bairus ke kara yaduwa a Nijeriya.

Mista Edward Kallon babban kodinata a sashin yada labarai na ofishin Majalisar Dinkin Duniya dake Nijeriya yace Majalisar Dinkin Duniya tare da kungiyar tarayyar Turai sun nuna matukar damuwa kan yadda annobar cutar Korona bairus ke yaduwa kamar wutar daji.

Ya ce tun bayan da aka fara samun billar cutar Korona bairus a Nijeriya an gargadi mahukunta dasu bada kulawa. Ya ce a lokacin al’umman qasar sun dauka abin wasane.

Ya ce yanzu yadda ake samun yaduwar cutar ta Korona bairus a Nijeriya abin sai adu’a.

Ya ce, lokacin da Majalisar Dinkin Duniya ta ga yadda lamarin yake a Nijeriya ta tallafawa qasar da bangaren kayan kariya da kuma magunguna dama malaman jinya.

Ya kara da cewa abin bakin ciki daga mutum daya aka fara a watan  Afirilu har ya kai mutum 6,677 kafin 20 ga watan mayu  sun kai 19,808.

Ya ce duk da matakin da Gwamnatin tarayyar Nijeriya ta dauka na matakan kariya da zaman gida da bin hanyoyin kariya amma abin ya gaza sakamakon sako sakon da wasu jihohin su kayi.

Ya ce Majalisar Dinkin Duniya da kungiyar tarayyar Turai suna kara taimakawa wajen bada matakan kare rayukan al’umma kasar.

Duk hanyoyin da zai kawo kariya domin kare rayuwar al’umman qasar da tallafi dabam dabam sunayi. Ya kara da cewa ya kamata a qara wayar da kan al’umma wajen kulawa da matakan kariya da hanyoyin dakile yaduwar cutar Korona bairus.

Saboda yanzu abin ya wuce tunani kuma kowani rana cutar qara yawaita ta keyi a tsakanin al’umman Nijeriya. Sakamakon gwaje gwajen cutar ya sanya dubannin mutani ake samu da cutar ta Korona bairus.

Ma’aikatar kiwon lafiya ta Nijeriya da Majalisar Dinkin Duniya tare da hadin kan tarayyar Turai zasuyi hadin giwa wajen wayar da kai masamman ga al’umman karkara dama biranai su gane hanyoyin da zasu iya kiyaye kamuwa da cutar da kansu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *