Gwamnan Nasarawa ya yabawa kungiyar NURTW

Gwamnan Nasarawa ya yabawa kungiyar NURTW
Daga Zubairu Lawal
Gwamnan Jihar Nasarawa Injiniya Abdullahi Sule ya yabawa kungiyar Motochin sufuri na NURTW reshen jihar Nasarawa.
Gwamnan Abdullahi Sule yace Kungiyar NURTW ta taka rawa wajen taimakawa Gwamnati a fannin baiwa matasa aikinyi.
Gwamnan Wanda ya samu wakilcin Sakataren Gwamnatin Jihar Alhaji Aliyu Ubandoma a wajen taron rantsar da sabbin Shugabannin kungiyar.
Yace; Gwamnati tana yabawa kungiyar saboda tana taimakawa wajen rage masu zaman kashe wando.
Yace; Gwamnatin Jihar Nasarawa ta duba matsalolin kungiyar akwai rashin dauwamamen matsuguni. Yace abaya cikin garin Lafia ko ina garejin motane.  Hakan ya sanya Gwamnatin ta gina tasoshin zamani guda biyu daya a Lafia daya a Karu.
Sannan yayi kira ga sabbin Shugabannin da suyi koyi da tsohuwar Gwamnatin da ta sauka karkashin Jagirancin Alhaji Salisu Adamu, domin ta taka mahimmiyar rawa wajen hadin kan membobin Kungiyar NURTW.
Shima Shugaban Jam’iyyar APC reshen jihar Nasarawa Alhaji Aliyu Bello ya jinjinawa membobin Kungiyar kan yadda suka gudanar da zaben ba tare da hamayya ba.
Yace; tsarin da shugabannin sukabi na kyautatawa membobi yake kara kawo biyayya tsakaninsu.
Tunda farko Shugaban Kwamitin da suka gudanar da harkokin zabe daga uwar kungiyar ta kasa. Karkashin Jagorancin Kwamared Idiris Adamu Abdullahi ta umarci tsohon Shugaban da ya rushe majalisar tsohuwar Gwamnatinsa kafin a rantsar da sabbi kamar yadda tsarin mulkin kungiyar NURTW ya tanada.
.Shugaban Kwamitin da ya jagorancin rantsarwa yace; Membobin kungiyar dake rassa 75 a fadin jihar sun aminci da zaben Membobin da zasu wakilcesu ba tare da hamayya ba.
Kwamarede Idiris Adamu Abdullahi ya kira yan takarar daya bayan daya inda ya tambayi ya’yan kungiyar ko sun amince dasu.
An rantsar da Sabon Shugaban kungiyar Alhaji Muhammad Abubakar Maikwarya tare da yan majalisanshi 24 da zasu aiki tare.
Sabon Shugaban kungiyar NURTW reshen jihar Nasarawa yayi godiya ga Membobin kungiyar da suka baiwa Shugabannin hadin kai suka zama tsintsiya madaurinki daya.
Alhaji Muhammad Abubakar Maikwarya ya jinjinawa tsohon Shugaban kungiyar Alhaji Salisu Adamu ya kuma yi alkawarin zai daura daga inda ya tsaya.
Tunda farko a jawabinsa na barin gado Tsohon Shugaban Kungiyar NURTW Alhaji Silisu Adamu Tafidan Masaka a jawabinshi, yayi godiya da Membobin kungiyar da suka bashi hadin kai har yakai ga cin nasara.
Ya kuma yabawa Gwamnan Jihar Nasarawa Injiniya Abdullahi Sule da ya taimakawa kungiyar wajen gina Tasoshin mota ta zamani a Lafia da Karu.
Yace; wannan ya hada kai NURTW wajen gudanar da ayyuka ba dare ba rana.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *