Kungiyar Fulani ta ratsar da Rundunar tsaro Dan samar da zaman lafiya a Kasa
Daga Zubairu Lawal
Shugaban Kungiyar Fulani makiyaya ta Kasa Dr. Alhaji Bello Abdullahi Bodejo ya jagoranci rantsar da Kungiyar yan Sintir da aka sanyawa suna ( NOMAD VIGINALTE NIGERIA).
Shugaban Kungiyar Miyetti Allah Kautal Hore na Jihar Nasarawa Alhaji Ardo Dahiru Dano ne ya ke jagorantar taron karkashin Shugaban kungiyar na ƙasa, Alhaji Dr. Bello Abdullahi Bodejo da nufin inganta tsaro da samar da zaman lafiya taron ya gudanane a Zauren taro na Ibrahim Abacha a Lafia jihar Nasarawa ranar Laraba.
Da yake jawabi Shugaban Kungiyar Miyatti Allah Kultal Hore na Kasa Dr. Alhaji Bello Abdullahi Badejo yace wannan shine karo na farko da kungiya ta samar da Kungiyar Fulani yan Sintiri da zasuyi aikin Sakai tare da Rundunar Jami’an tsaro ta Kasa domin tabbatar da zaman lafiya mai dorewa a Kasa.
Wadannan yan Sintiri 1,144 na jihar Nasarawa da zasuyi aiki tare da Rundunar Mahukunta a Kananan hukumomi 13 dake fadin jihar domin samar da zaman lafiya.
Yace: duk da cewa adadin matasan sun kai kimanin 4,000 zasuyi aiki tukuri domin tabbatar da zaman lafiya.
Yace; Kungiyar Fulani ta Miyatti Allah ta yanke shawarar samar da Jami’an sintirine domin taimakawa Gwamnati a samu zaman lafiya a Kasa baki daya.
Yace; wannan Rundunar zata kewaye ko ina a fadin Kasa, kuma zasu taka mahimmiyar rawa wajen tabbatar da zaman lafiya a Nijeriya.
Ya qara da cewa yana da kwarin giwa kan wannan Rundunar ta yan Sintiri cewa zasu taimakawa jami’an tsaro a yake gurbatatu dake addaban al’umman Kasa.
Ya gargade yan Sintirin dasuyi aiki tsakani da Allah wajen kawo karshe yan ta’adda a kowani guri da sukaji labarai koda Jami’an tsaro bazasu iya shiga ba su sakai Allah zai taimakesu.
Bayan taron Shugaban Kungiyar Fulani ta Miyatti Allah ya jagoranci Rundunar yan Sintiri zuwa ofishin kwami shinan yan Sanda na jihar Nasarawa.