KAKAKIN MAJALISAN DOKOKIN YA YABAWA SHUGABAN KASA BUHARI DA GWAMNAN NASARAWA SABODA AYUKAN ALHERI

Kakakin Majalisar Nasarawa ya yabawa shugaba Buhari da Gwamna Abdullah Sule

Daga Zubairu M Lawal

Kakakin Majalisar dokokin jihar Nasarawa Honorabul Balarabe Abdullah ya yabawa Shugaban kasa Muhammad Buhari Dan gane da irirn kyakyawar kudduri da yake tafiyar da ita a kasa.

Kakakin Majalisar ya ce hakika alumman Nijeriya suna ganin Shugabanci mai amfani. Ya Shugaban qasar na ayyukan cigaba da samar da zaman lafiya da hada kan yan qasa su zaman masoyan juna.

Ya ce anga sauyi mai yawa tun daga hawan mulkin Shugaba Muhammad Buhari. Kuma yan Nijeriya suna murna da nuna goyon baya.

Haka zalika Kakakin Majalisar ya yabawa Gwamnan jihar Nasarawa Injiniya Abdullah Sule Dan gane da cigaban da ya samar cikin shekara daya da kama Gwamnatin sa.

Ya ce , cikin kankanin lokaci alumman jihar Nasarawa sun amfana da abubuwa mai yawa. Honorabul Balarabe ya yabawa Gwamnan Abdullah Sule yadda ya dukufa wajen kammala manyan ayyukan cigaba da tsuhuwar Gwamnati ta tafi ta bari.

Kamar filin sauka da tashin jiragen sama da ake ginawa a Kwandare da hanyoyin karkara da biranai. Yace haka ake bukatar Shugaba na kwarai da yaga aiki yayi kokarin kammala shi ba tare da bata lokaci ba.

Kakakin Majalisar dokokin jihar ta Nasarawa yayi kira ga alumman jihar da su kara baiwa Gwamnatin Injiniya Abdullah Sule goyon baya Dan cigaba. Kuma ya bukaci su baiwa gwamnati hadin kai wajen yaki da yaduwar Annobar cutar Korona da ta addabi kasan nan da duniya baki daya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *