TALAKAWA SUN JAHILCI CUYAR COVID-19 A TARAYYAR NIJERIYA
Inji Dakta Tijani Hussaini
Daga Adam Zubair
Kwararen masani a fannin binciken cututuka a jihar Kano Dakta Tijjani Hussaini ya bayyana yadda al’umma suka kadu masamman Talakawa.
Ya ce wasu ma’aikatan lafiya a Kano wadanda suka kamu da cutar covid-19, sun tayarma da Talakawan jihar kano hankali.
Duk da cewa da yawan Talakawan jihar Kanon ba su yarda da wannan cuta ba, amma kamuwar likitocin da suka yi, ya tayarma da talakawan hankali, kuma ya sa sun shiga taitayin su game da cutar.
Ya ce rashin yin amana da cutar tun farko ya sanya yanzu cutar take ta yaduwa cikin jama’a. Ya ce a lokacin da cutar ta shigo tarayyar Nijeriya ana gargadin mutani amma dayawa sunyi kememe saboda suna tunanin cutar ba gaskiya bane.
Wasu ma na danganta annobar cutar Korona bairus da cewa cuta ce ta masu mulki da masu dukiya.
Dakta Tijjani Hussaini yace an dade ana gargadin al’umman cikin birnin Kano masamman mazauna yankin Dorayi da Zango da Gwale gurare ne da akafi yawan cin koso, amma mutani sun ki bin shawarwarin malaman kiwon lafiya.
Hukuma kula da lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya dake tarayyar Nijeriya sun gargadi da ba da shawarwari ga al’umman Nijeriya amma daya talakawa sun ki amincewa suna gani wasa ne.
Kamuwar wasu Likitoci ya sanya dayawa Talakawa suka fara dawowa cikin hayacinsu. Ya qara da cewa cutar yanzu ta shiga lungu da sako tana kara yaduwa cikin al’umma.
Yanzu da ake gwaje gwajen cutar Korona bairus gashi kullun sai yawaita akeyi. Ya kuma shawarci mutani dasu daina jin tsoro su rika gwaje gwajen cutar saboda a san masu ita ayi masu magani cikin sauki ba tare da sun cigaba da yadata zuwa ga danginsu ko abokan harkokin su ba.