GWAMNATIN TARAYYA TA BA DA UMURNIN BUDE SANSANONIN NYSC
Gwamnatin tarayya ta amince a bude cibiyoyin hidimar kasa wato NYSC a duk fadin kasar. Sanarwar ta fito ne daga babban jami’in kwamitin karta kwana na fadar shugaban kasa dake kula da yaduwar cutar Korona, Dr. Sani Aliyu, inda ya shaidawa manema labarai hakan a yayin wata tattaunawa a filin jirgin sama na Nmandi Azikwe dake Abuja.
Ya kara da cewa ya zama wajibi al’umma da sauran masu ruwa da tsaki, da su maida hankali wajen ci gaba da dabbaka matakan dakile yaduwar cutar ta Korona a fadin Najeriya.