Gwamnatin jihar Bauchi ta rungumi kuddurin dokan VAPP
Daga Zubairu M Lawal
Gwamnatin jihar Bauchi itace jihar ta farko da ta fara rungumar kaddamar da shirin dokar VAPP dake yaki da tauye haki da cin zarafin mata.
Kuddurin da vangaren Mata na Majalisar Xinkin Duniya tare da Gwamnatin kasar Ingila suka kaddamar da kwamtin mai kulla da zai zartar da dokokin da zai hana cin mutumcin mutani masu rauni,.
Tun a watan hudu na shekara ta 2021 aka samar da kwamitin da suka zantar da dokokin.
Jihar Bauchi sune na farko a shiyar Arewa maso gabas Wanda suka soma zartar da dokar VAPP. Shine Sabin doka da zai dinga Jin baasi akan cin mutuncin mata da Gwamnatin jahar Bauchi ta sauka nauyi, da kuma kudiri ganin ansamu cigaba da Zaman lafiya da tsaro a jahar Bauchi baki daya.
Shi dai wannan shirin zartar da dokar cin zarafin mata zai koyar da dabaru wajen ganin an dakile duk wani aukuwar hakan a jahar Bauchi.
A wajen taron, mai Girma Gwamnan Jihar Bauchi Bala Abdulkadir yace; Jiharsa a shirye take ta aiwatar da dokar don ganin an hukunta masu yin haka.
Kuma yace zartar da dokar VAPP tabbas zai samu goyon baya daga yan siyasa na wannan Jihar tamu kuma zamu sanya hannu da zaran angama shirya dokar na VAPP.
Saboda haka jihar ta Bauchi tana wani shiri na ganin an taimaki wadanda ke cikin wani hali da Samar da walwala ga mata. Mungode sosai da hadin kai da goyon baya da kuka bamu. Inji Gwamna Bala Muhammad.