Cin koson mutani a gidajen yari barazana ne ga bangaren shari’a Inji Labaran Magaji

Cin koson mutani a gidajen yari barazana ne ga bangaren shari’a
Inji Labaran Magaji
Daga Zubairu .Lawal
Cin koson mutani a gidajen yari barazana ne ga bangaren Shari’a.
kwamishinan Shari’a Barrister Labaran Magaji yace; kuddurin Gwamnatin Injiniya Abdullahi Sule shine samar da dauwamameyar zaman lafiya da hukunta duk wani mai lefi ta hanyar shari’a.
Saboda haka Ma’aikatar Shari’a ta daukarwa kanta nauyin ziyarartar bangaren hukumomin dake da alaqa da Shari’a
Kwamishinan yace; yiwa mai lefi hukuncin akan lokaci adalcine bai kamata ace cikoson mutani suna zaune a gidar waqafi suna jirar shari’a tsawon lokaci ba.
Ya qara da cewa Gwamna Abdullahi Sule mutumne mai buqatar ganin ayiwa kowa adalci dan haka zasu waiwayi bangaren mutanin da aka barsu batare da sanin  matsayisu ba a gidajen yarin.
Barrister Labaran Magaji yace; zasu samar da tsare tsare  domin tsaftace gidajen gyara hali da aka dasu a fadin jihar ta hanyar rage cinkoso.
Tun da farko Shugaban hukumar kula da gidajen yarin jihar Nasarawa ( Nigeria Correctional Service) Mr. Yunusa A. Ibrahim ya shedawa Kwamishinan Shari’a na jihar Nasarawa Barrister Labaran Shuaibu Magaji halin cinkoson da ake fama da shi a gidajen yarin  sakamakon jan kafa wajen gudanar da  shari’a.
A ziyarar da Kwamishin Shari’ar ya kai zuwa Ofishin Shugaban Hukumar kula da gidajen yarin. Da nufin hadin kai domin gudanar da aiki tare masamman wajen ganin an kawo karshen rage lefuka a jihar.
Mr. Yunusa A. Ibrahim ya bayyana damuwarsa kan yadda ake Jan kafa wajen gudanar da Shari’ar mutanin da ake zargi da aikata lefuka a jihar Nasarawa.
Yace;  gidajen yari dake jihar Nasarawa ya cika da mutani a sakamakon rashin yiwa da dama shari’a da zasu san matsayinsu.
Yace adadin mutum 1,321 ake da matsuguninsu a gidajen yarin dake fadin jihar da suka hada da Lafia, Wamba, Keffi, Nasarawa.
Amma yanzu akwai mutum 2069 da yawansu ya haifar da cin koson mutani a gidajen yarin.
cikinsu masu zaman jirar Shari’a sun kai 1408. Amma wadanda aka yankewa hukunci 640.
Ya roki Kwamishinan Shari’ar da ya sanya baki ga kotun dasu rika gabatar da Shari’a akan lokaci domin zai rage cin koson jama’a a gidajen yari

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *