Nasarar Gwamna Abdullahi Sule na Al’umman Nasarawa ne – APC

Nasarar Gwamna Abdullahi Sule na Al’umman Nasarawa ne – APC
Daga Zubairu Lawal
Jami’iyyar APC mai mulki a jihar Nasarawa ta bayyana nasarar da Gwamna Abdullahi Sule ya samu a kotun daukaka kara kan jam’iyyar PDP a Abuja da cewa nasara ce ga al’umman jihar Nasarawa.
Cikin takardan da Jami’in hulda da manema Labarai na jam’iyyar APC Mr. Otaru Douglas ya fitar tana dauke da bayyana murna da farin ciki da nasarar da shari’a tabayyawa jam’iyyar APC.
Yace; jam’iyyar APC a jihar Nasarawa tana tafiya ne uwa daya uba daya. Yace; jam’iyyar tana hada kan al’umman jihar Nasarawa shiyasa a lokacin da kotun farko ta kwace zabe al’umman jihar Nasarawa sun shiga halin damuwa.
Yayi kira ga mutanin jihar Nasarawa dasu gudanar da murna da farin ciki a nutsuwa banda hayaniya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *