Wajibi ne a samu kyakyawar dangan taka tsakanin yan jarida aalumman Nijeriya .
Inji Edward Kallon
Daga Zubairu M Lawal
Majalisar dinkin Duniya ta bukaci kafafen yada labarai da su kara samun jituwa tsakanin su da Jama’a a Najeriya.
Mista Edward Kallon yace ; maka su din wanan taron na wayar da kai da majalisar Dinkin Duniyar ta shirya ma ‘yan jaridan dan ganin an sabinta yanayin dangantakar da ke tsakanin manema labaran da sauran dimbin Al’umar da ke sauraren su.
Domin a nuna ma ‘yan jaridan yadda za su ci moriyar sababbin hanyoyin isar da sako ga Al’umma na wannan zamanin da ake ciki. Kuma dole ne ‘yan jaridan su dinga ilimantar da masu saurarensu ta sabowar hanyar nan da ake kira da (MIL) a takai ce.
Yace; yanzu an samu cigaba wajen gudanar da aikin jarida , alumma suna gudanar da kyakyawar mu’amala da yan jaridu . wani lokacin mutani sukan kira yan jarida su basu labarin da basu sani ba.
Mista Edward Kallon yayi kira ga yan jarida da su rika tabbatar da sashi hancin labari kafin su wallafa shi.
Haka Kuma su zamo masu binchike da kwakwarar hujja da zai gamsar da masu saurare.yace ; aikin jarida aikine dake wayar da kan mai yin ta. Kuma yan jarida suke wayar da kan alumma.
Saboda sune ke fadawa alumma abubuwan da ke faruwa Kuma suke bayyana abin da aka boye ba ason ya bayyana. Ya qara da cewa a ko ina ana alfahari da yan jarida saboda kowa yana son karanta jarida matasa Malamai maza da mata kowa na qaruwa da aikin jarida .
Taron da ya gudana a zauren taro na majalisar Xinkin Duniya ya samu halartan hamsin da biyu daga gidajen jaridu arba’in da uku.
Haka zalika taron ya tara dalubai masu karatun koyon aikin jarida daga manyan makarantun .